Hana Yara Cin Sukari da Yawa Kafin Su Kai Shekara Biyu Na Iya Kare Ƙwaƙwalwarsu Idan Sun Tsufa — Bincike

DA DUMI-DUMI

Rage Cin Sukari Kafin Shekara Biyu na Iya Taimakawa Wajen Kare Ƙwaƙwalwa Daga Cutar Mantuwa -Bincike

Wani sabon bincike ya nuna cewa rage yawan sukari da yara ke ci kafin su cika shekara biyu na iya taimakawa wajen rage haɗarin kamuwa da cutar mantuwa (dementia) a lokacin tsufa.

Masu binciken sun yi nazarin bayanan mutane kusan 65,000 daga shirin UK Biobank, inda suka kwatanta mutanen da aka haifa lokacin da ake takaita amfani da sukari a Birtaniya bayan Yaƙin Duniya na Biyu da waɗanda aka haifa bayan an kawo ƙarshen tsarin a shekarar 1953.

Sakamakon binciken ya nuna cewa mutanen da suka taso a lokacin da ake takaita sukari har zuwa shekara biyu sun kasance da kashi 23 cikin 100 ƙasa da haɗarin kamuwa da cutar dementia. Haka kuma, idan sun kamu da cutar, tana bayyana ne kusan shekaru biyu da rabi a makare idan aka kwatanta da sauran mutane.

Jagorar binciken, Jiazhen Zheng daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Hong Kong da ke Guangzhou, ya ce binciken ya nuna cewa rage sukari a farkon rayuwa na iya kawo fa’ida ga lafiyar ƙwaƙwalwa a nan gaba, sai dai ya jaddada cewa ana buƙatar ƙarin bincike domin tabbatar da alaƙar.

Sai dai masana masu zaman kansu sun yi gargaɗin cewa binciken na nuna alaƙa ne kawai, ba ya tabbatar da cewa rage sukari kai tsaye ne ke hana kamuwa da dementia.

Masana sun kuma ce, duk da haka, cin abinci mai gina jiki da daidaitaccen tsarin abinci na daga cikin muhimman hanyoyin da ke taimakawa wajen kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da rage haɗarin kamuwa da cututtukan tsufa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img