Sarkin Musulmi: Kada A Yi Wa Fulani Duka Laifin Ƴan Ta’adda
Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina kiran masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da sunan Fulani makiyaya, yana mai cewa duk wanda ya aikata laifi a kira shi mai laifi, ba tare da danganta shi da wata ƙabila ba.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin buɗe taron ƙasa na shekarar 2026 na Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da aka gudanar a Abuja.
Ya ce bai kamata a hukunta ko a ɗora wa miliyoyin Fulani masu zaman lafiya laifin wasu tsirarun masu aikata laifuka ba.
“Ku kira su masu laifi kawai. A kowace iyali akwai nagari kuma akwai marasa kyau. Ni ina cikin iyalan nagari,” in ji Sarkin Musulmin.
Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya kuma tabbatar da cewa al’ummomin Fulani a shirye suke su yi aiki tare da gwamnatin tarayya da jami’an tsaro domin gano tare da fatattakar masu laifi daga yankunansu.
Haka kuma, ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kafa Ma’aikatar Raya Kiwo ta Tarayya, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen bunƙasa harkar kiwo da ci gaban masana’antar dabbobi a Najeriya.
A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Othman Ngelzarma, ya yi Allah wadai da ta’addanci, garkuwa da mutane, fashi da makami da satar shanu, yana mai jaddada cewa bai dace a jingina laifukan wasu tsirarun mutane da wata ƙabila, addini ko sana’a ba.
Ya ce MACBAN za ta ci gaba da ƙarfafa mambobinta su bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai tare da yin watsi da duk wani nau’in aikata laifi.




