Macron Ya Bar Tinubu A Faransa, Ya Nufi Taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York, Amurka

DA DUMI-DUMI

Macron Ya Bar Tinubu A Faransa, Ya Nufi Taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York, Amurka

Daga Wakiliya

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya bar birnin Paris zuwa New York domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

Taron zai fara ne a ranar Talata, 22 ga Satumba, inda shugabannin ƙasashe daga sassan duniya za su taru domin tattauna batutuwan da suka shafi duniya.

A yayin da Macron ya nufi New York, Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ci gaba da kasancewa a Faransa saboda hutun da yake yi.

Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron. Kuma tuni har Shettima ya riga ya isa New York, kuma zai gabatar da jawabin Najeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniyar.

Wannan shi ne karo na uku a jere da Shettima zai wakilci Tinubu wajen gabatar da jawabin Najeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Shettima ya wakilci Tinubu a tarukan 2024 da 2025, yayin da Tinubu da kansa ya halarci taron na 2023 amma daga nan bai sake zuwa ba.

A bana, taron zai mayar da hankali kan batutuwa daban-daban da suka shafi duniya, ciki har da rikice-rikice, sauyin yanayi, fasahar AI da kuma sauye-sauyen da ake bukata a tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img