Na Cika Alkawuran Da Na Ɗauka, Tattalin Arzikin Najeriya Ya Fara Daidaita – Tinubu

DA DUMI-DUMI

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cika muhimman alkawuran da ta ɗauka tun bayan hawanta mulki, yana mai cewa tattalin arzikin Najeriya ya fara samun daidaito bayan sauye-sauyen da aka aiwatar.

Tinubu ya ce duk da ƙalubalen da aka fuskanta a farkon aiwatar da manufofin gyaran tattalin arziki, yanzu alamu sun fara nuna cewa ƙasar na komawa kan turbar bunƙasa.

Shugaban ƙasar wanda ke jawabi a yayin da ya karbi tawagar mutanen Arewa Maso Yamma da suka ziyarce shi a fadarsa ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da za su ƙarfafa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Ya kuma buƙaci ‘yan ƙasa da su ci gaba da nuna haƙuri da goyon baya, yana mai cewa sakamakon sauye-sauyen da aka fara zai ƙara bayyana a cikin lokaci.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img