Ɗan Majalisa Ya Ce Wani Abokin Aikinsa Ya Kasa Biyan Kuɗin Makarantar ‘Yarsa Na Naira 700,000
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar AMAC/Bwari a Abuja, Chinedu Obika, ya bayyana cewa kimanin watanni biyu da suka gabata wani ɗan majalisa abokin aikinsa ya kasa biyan kuɗin makarantar ‘yarsa har Naira 700,000, lamarin da ya sa shi ya taimaka ya biya.
Obika ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka wallafa a shirin KAA Truths, inda yake mayar da martani kan zargin da ake yi cewa ‘yan Majalisar Tarayya na karɓar kuɗaɗe masu yawa.
A cewarsa, wannan ya nuna cewa ba dukkan ‘yan majalisa ne ke cin gajiyar abin da jama’a ke kallon “wadatar kuɗi” a Majalisar Dokoki ba.
Ya kuma ce wasu ‘yan majalisar da ba sa yawan magana a zauren majalisa ba wai saboda ana ba su wani abu ba ne, illa saboda ba su da wani abin da za su nuna daga mukamansu.
Sai dai Obika bai bayyana sunan ɗan majalisar da ya ce ya taimaka wa wajen biyan kuɗin makarantar ‘yarsa ba.
Hakazalika, ya jaddada cewa dukkan haƙƙoƙi da alawus-alawus da ‘yan Majalisar Tarayya ke samu a bayyane suke, tare da ƙalubalantar ‘yan Najeriya su riƙa gabatar da hujjoji kan duk wata magana da ake yi game da albashinsu da alawus-alawus maimakon jita-jita.





