“Muna da fayil-fayil na malaman addini da yawa a hannunmu” – Shugaban EFCC, Olukoyede
Daga Wakiliya
Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC, Olanipekun Olukoyede, ya ce hukumar na da dimbin fayilolin shari’ar wasu fastoci da limamai da ake zargi da aikata laifukan kuɗi.
Olukoyede ya ce wasu daga cikin mutanen da ke cikin waɗannan fayiloli har an same su da laifi kuma suna zaman gidan yari.
Ya bayyana hakan ne a wajen taron Majalisar Ƙasa kan Huldar Addinai, NIREC, da aka gudanar a Abuja.
Shugaban EFCC ya ce bai kamata a yi amfani da mukaman addini kamar “Fasto” ko “Limami” a matsayin kariya daga bincike ko hukunta mutum ba.
Ya ce abin da ya kamata ya nuna sahihancin malamin addini shi ne ayyukansa da halayensa, ba sunan da yake amfani da shi ba.
Olukoyede ya kuma yi gargadin cewa hukumar ba za ta yi wa wani sassauci ba saboda matsayinsa na addini idan ya aikata laifin kuɗi.




