Amnesty ta zargi gwamnatin Kano da musgunawa masu sukar ta
Daga Wakiliya
Ƙungiyar Amnesty International ta zargi gwamnatin Jihar Kano da hannu wajen kamawa, tsarewa da kuma tsoratar da mutanen da ke sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Amnesty ta ce wasu mutane sun fuskanci kamawa ko gayyata daga hukumomin tsaro sakamakon kalaman da suka wallafa a kafafen sada zumunta.
Ƙungiyar ta ambaci Abba Ibrahim Kofar Nasarawa, wanda aka fi sani da Aiha K Nass, da Murtala Muhammad Dawanau da Fatima Dayyabu, da wasu mutane da dama.
Amnesty ta ce irin waɗannan matakai na kawo cikas ga ‘yancin faɗar albarkacin baki a Kano, tare da kira ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro su mutunta ‘yancin jama’a na sukar shugabanni.
Sai dai gwamnatin Kano ta ƙaryata zargin, tana mai cewa bayanin Amnesty akwai son kai kuma bai yi la’akari da cikakken bayani ba.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Waiya, ya ce ‘yancin faɗar albarkacin baki yana da kariya a kundin tsarin mulki, amma hakan ba ya bai wa mutum kariya daga bincike ko gurfanar da shi idan ya karya doka.
Gwamnatin ta ce ya kamata a duba kowanne daga cikin shari’un daban-daban bisa zarge-zargen da ake yi, hujjojin da aka gabatar da kuma hukuncin kotuna.




