Kotu ta tabbatar da Pantami halastaccen dan PDP ne, Amma ta umarci a sake zaɓen fidda gwani a Gombe

DA DUMI-DUMI

Kotu ta tabbatar da Pantami halastaccen dan PDP ne, Amma ta umarci a sake zaɓen fidda gwani a Gombe

Daga Wakiliya

Kotun Tarayya da ke Gombe ta tabbatar da cewa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami halastaccen ɗan jam’iyyar PDP ne, tare da umartar jam’iyyar da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani na kujerar gwamnan jihar.

Kotun ta ce dole ne a sake gudanar da zaɓen cikin wata guda, bayan da ta gano cewa PDP ba ta sanar da wasu daga cikin ‘yan takarar da aka cire daga takarar ba yadda ya kamata.

An bayyana Pantami a matsayin ɗan takarar PDP a zaɓen fidda gwani na ranar 26 ga Mayu 2026, bayan an cire wasu masu neman takarar.

Sai dai Hamma Sale, Khamis Mailantarki da Usman Aliyu sun kalubalanci tsarin a kotu.

Kotun ta yi watsi da ƙarar Hamma Sale, amma ta ce PDP ta sake gudanar da zaɓen, tare da bai wa Pantami, Mailantarki da Usman damar shiga sabon zaɓen.

Har yanzu PDP ba ta bayyana ranar da za a gudanar da sabon zaɓen fidda gwani ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img