Mun Bai Wa Tinubu Nasara a 2023, Yanzu Olawepo-Hashim na jam’iyyar Accord Za Mu Zaba a 2027 -inji Yan Arewa

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Wasu tsofaffin jiga-jigan jam’iyyar APC da magoya bayanta a jihohin Kano, Jigawa da Katsina sun bayyana goyon bayansu ga jam’iyyar Accord da ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2027, Dakta Gbenga Olawepo-Hashim.

A tarukan gangamin da aka gudanar a jihohin uku, mahalarta sun ce matsin tattalin arziki, rashin tsaro da rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da mulki ne suka sa suka yanke shawarar komawa wata jam’iyya.

Jagorar Mata ta Hashim Progressive Movement, Ambasada Aisha Ibrahim, ta ce sun taka rawa wajen nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023, kuma yanzu suna shirin yin irin wannan aiki domin Gbenga Hashim a 2027.

Ta ce, “Mun yi alkawarin ba Tinubu nasara a 2023 kuma mun cika. Yanzu muna alkawarin ba Gbenga Hashim nasara a 2027, kuma da yardar Allah za mu cika.”

Wasu daga cikin masu jawabi sun bayyana cewa sun fice daga APC ne saboda halin ƙuncin rayuwa da matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.

Wakilan Olawepo-Hashim sun ce ƙungiyar na ci gaba da faɗaɗa gangamin wayar da kai a faɗin Najeriya, tare da jaddada cewa manufofinsa sun haɗa da farfaɗo da tattalin arziki, inganta tsaro, samar da ayyukan yi da bunƙasa walwalar jama’a.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img