Maraban JOS:  Amnesty Ta Zargi ‘Yan Sanda da Yiwuwar Rufe Gaskiya a Kisan Ummulkhair

DA DUMI-DUMI



Daga Wakiliya

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano gaskiyar abin da ya faru a kisan gillar da aka yi wa Ummulkhair, malama kuma uwa ga yara biyar.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana cewa ba za a iya dogaro da binciken da rundunar ‘yan sanda ta ce tana yi ba, musamman ganin cewa akwai zarge-zargen cewa wasu jami’an ‘yan sanda sun taka rawa wajen mika marigayiyar ga taron mutanen da suka kashe ta.

Amnesty ta ce shaidu sun bayyana mata cewa lokacin da jama’a suka mamaye ofishin ‘yan sanda a ranar 21 ga Yuni, jami’an da ke bakin aiki sun fitar da Ummulkhair daga wurin da ake bata kariya, suka cire mata hijabi sannan suka mika ta ga masu tarzoma, inda suka kashe ta tare da kona gawarta.

Ƙungiyar ta ce ci gaba da yawaitar kashe-kashen gilla a Najeriya alama ce ta gazawar gwamnati wajen kare rayuka da tabbatar da adalci. Ta kuma zargi jami’an tsaro da gaza bincike da hukunta masu hannu a irin waɗannan laifuka a lokuta da dama.

Amnesty International ta jaddada cewa dole ne a gudanar da bincike na gaskiya, adalci da cikakken ‘yanci domin tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aika.

Rahoton – Wakiliya

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img