Babban Albishir Ga Arewa: An Gano Manyan Ma’adanai Masu Daraja a Kaduna -FG

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da gano manyan ma’adanai masu daraja a jihar Kaduna, ciki har da Platinum, Lithium, Zinariya, Nickel, Copper da kuma Rare Earth.

An ce waɗannan ma’adanai na daga cikin mafi muhimmanci a duniya saboda ana amfani da su wajen ƙera batirin motocin lantarki, wayoyin salula, kwamfuta, na’urorin zamani, injina, da kuma wasu kayan aikin masana’antu.

Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ya ce binciken ya nuna cewa Kaduna na ɗaya daga cikin wuraren da ke da manyan ma’adanan da za su iya jawo zuba jari, samar da ayyukan yi, da kuma bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.

Sai dai masana na jaddada cewa abin da zai fi amfani shi ne sarrafa waɗannan ma’adanai a cikin Najeriya, maimakon fitar da su ƙasashen waje ba tare da an ƙara musu ƙima ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img