Ina Fatan Wata Rana A Samu Kirista da Kirista Su Mulki Najeriya Kamar Yadda Aka Samu Muslim-Muslim – Gwamna Sule

DA DUMI-DUMI

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce yana fatan wata rana Najeriya za ta samu tikitin shugaban ƙasa da mataimakinsa duka Kiristoci, kuma ya yi nasara a zaɓe.

Abdullahi Sule ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda yake mayar da martani kan kalaman ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, game da yiwuwar sake tsayar da tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen 2027.

Gwamnan ya ce tikitin Musulmi da Musulmi ba yana nufin wariya ta addini ba, yana mai cewa a tarihin Najeriya an taɓa samun irin wannan tikiti a zaɓen 1993 ƙarƙashin marigayi MKO Abiola, kuma ya yi nasara.

Ya kuma ce yana addu’ar ganin wata rana da za a gwada tikitin Kirista da Kirista, yana mai fatan shi ma zai samu nasara a zaɓe.

Abdullahi Sule ya ƙara da cewa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya fi mayar da hankali kan wakilcin yankuna da ƙabilu ta hanyar tsarin federal character, ba tare da ya tanadi wani sharadi na daidaita addini ba.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa tun lokacin da ya hau mulki yana aiki tare da mataimakinsa, Emmanuel Akabe, wanda Kirista ne, yana mai cewa an zaɓe shi ne saboda ƙwarewarsa, ba don daidaita addini ba. Ya ƙara da cewa tsarin siyasa ya kan bambanta daga jiha zuwa jiha.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img