Masu son a dawo da tallafin man fetur ba sa nufin ku da alheri – Gwamna Otti

DA DUMI-DUMI

Masu son a dawo da tallafin man fetur ba sa nufin ku da alheri – Gwamna Otti ya gargadi yan Najeriya 

Daga Wakiliya 

Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya ce masu neman a dawo da tallafin man fetur ba sa yi wa Najeriya fatan alheri.

Otti ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce cire tallafin man fetur mataki ne da ya dace, duk da wahalhalun da jama’a suka fuskanta.

Ya ce tallafin amfani da man fetur ya fi amfanar wasu tsirarun mutane, maimakon taimaka wa tattalin arzikin ƙasa.

Gwamnan ya ce ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali wajen tallafa wa samar da kayayyaki da ayyukan tattalin arziki, maimakon tallafa wa amfani da su.

Ya kuma bayyana tsarin tallafin man fetur na baya a matsayin wani tsari da ya bude damar amfani da dukiyar jama’a ba bisa ka’ida ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img