Gwamnatin Tarayya na son ta rika biyan dubu N150,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi amma Gwamnoni sun hana – HoCSF Goni

DA DUMI-DUMI



Daga Wakiliya

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (HoCSF), Alhaji Bukar Goni, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya a shirye take ta biya ma’aikata mafi ƙarancin albashi na ₦150,000, amma gwamnatocin jihohi, ƙananan hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu sun nuna ba za su iya ɗaukar nauyin hakan ba.

Goni, wanda ya jagoranci kwamitin tattaunawar mafi ƙarancin albashi, ya ce jihohi da ƙananan hukumomi sun bayyana cewa ba su da ƙarfin biyan wannan adadi, yayin da kamfanoni masu zaman kansu suka yi gargaɗin cewa za su rage ma’aikata idan aka tilasta musu biyan hakan.

Ya yi kira da a gyara Kundin Tsarin Mulkin 1999 domin a cire batun mafi ƙarancin albashi daga jerin abubuwan da tarayya da jihohi ke da hurumi a kansu tare, domin kowace gwamnati ko ɓangare ya rika biyan albashi gwargwadon ƙarfinsa.

A wani ɓangare, Goni ya nuna damuwa kan rashin haɗin kai tsakanin hukumomin gwamnati da jami’an tsaro, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga yaƙi da ta’addanci da kuma gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

Ya kuma yi kira da a sake fasalin manhajar ilimi ta Najeriya domin ta dace da bukatun ƙarni masu zuwa, tare da jaddada cewa babu wani gyara da zai yi tasiri ba tare da isasshen kuɗi ba.

Rahoton ya fito ne yayin wani taron bikin Ranar Ayyukan Gwamnati ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta 2026 da aka gudanar a Abuja.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img