Majalisar Kwara ta soke kujerun ’yan majalisa biyu saboda sun fice daga jam’iyyar APC

DA DUMI-DUMI

Majalisar Kwara ta soke kujerun ’yan majalisa biyu saboda sun fice daga jam’iyyar APC

Daga Wakiliya

Majalisar Dokokin Jihar Kwara ta bayyana kujerun ’yan majalisa biyu a matsayin babu kowa, bayan sun fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

’Yan majalisar da lamarin ya shafa su ne Saaba Yisa Gideon, mai wakiltar mazabar Edu, da kuma Olushola Odetundun, mai wakiltar mazabar Irepodun.

Majalisar ta dauki matakin ne yayin zaman ta, bayan shugaban jam’iyyar APC na jihar, Prince Sunday Fagbemi, ya bukaci a yi amfani da tanadin sashe na 109(1)(g) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.

A wasikar da ya aikewa Kakakin Majalisar, Salihu Yakubu Danladi, Fagbemi ya ce ’yan majalisar sun rasa damar ci gaba da zama a kujerunsu, saboda sun bar jam’iyyar da aka zabe su a karkashinta, suka koma PDP.

 

Me kundin tsarin mulki ya ce?

Da yake jagorantar muhawara kan batun, shugaban masu rinjaye na Majalisar, Oba Mogaji, ya ce batun na da nasaba da kundin tsarin mulki.

Ya ce sashe na 109(1)(g) ya tanadi cewa dan majalisa zai iya rasa kujerarsa idan ya sauya jam’iyya bayan an zabe shi, sai dai a wasu yanayi da kundin tsarin mulkin ya tanada.

Mogaji ya ce Gideon da Odetundun an zabe su ne a karkashin APC, amma daga bisani suka koma PDP, inda suka samu tikitin jam’iyyar na tsayawa takarar zabukan cike gurbi da za a gudanar a mazabunsu.

Wasu ’yan majalisar, ciki har da Abolarin Ganiyu Gabriel na Ekiti, Ganiyu Folabi na Omupo da Adato Oguniyi na Ojomu/Balogun, sun goyi bayan matakin.

Daga bisani Kakakin Majalisar, Salihu Yakubu Danladi, ya sanar da cewa kujerun mazabun Edu da Irepodun sun zama babu kowa.

 

PDP ta yi tir

Jam’iyyar PDP a Kwara ta yi watsi da matakin, tana zargin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da Kakakin Majalisar da amfani da majalisar wajen hukunta ’yan majalisar saboda zabin da suka yi na sauya jam’iyya.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na jihar, Olusegun Olusola Adewara, ya fitar, PDP ta bayyana lamarin a matsayin abin da ka iya jefa siyasar jihar cikin rashin jituwa.

Jam’iyyar ta ce ’yan majalisar suna da ’yancin sauya sheka zuwa wata jam’iyya, kuma bai kamata a dauki hakan a matsayin rashin da’a wajen gudanar da aikinsu na majalisa ba.

PDP ta ce ’yan majalisar biyu sun samu afuwar kwamitin gudanarwa na jam’iyyar a jihar, sannan suka samu tikitin PDP domin fafatawa a zabukan cike gurbin da ke tafe.

Jam’iyyar ta kuma ce cire ’yan majalisar na iya hana al’ummar mazabun Edu da Irepodun samun cikakkiyar wakilci a majalisar.

PDP ta amince cewa Majalisar na da ikon tsara yadda za ta gudanar da harkokinta karkashin sashe na 101 na Kundin Tsarin Mulki, amma ta ce wannan iko bai kamata ya wuce iyakokin kundin tsarin mulki ba.

Jam’iyyar ta ce za ta yi amfani da “dukkan hanyoyin doka da kundin tsarin mulki” wajen kalubalantar matakin.

Ta kuma bukaci Kakakin Majalisar, wanda PDP ta ce yana neman takarar gwamnan jihar a karkashin APC, da ya nuna hakuri da bambancin ra’ayin siyasa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img