Zainab ta yi “blocking” ɗin makaniken motarta bayan ta lura yana yawan kallon Status ɗinta — “Ba kowa ya kamata ya riƙa bibiyar Status ɗinmu ba,” inji ta
Daga Wakiliya
Fitacciyar yar Gwagwarmaya daga Kano wacce ake yiwa take da Jagorar Talakawa, Zainab Nasir Ahmed ta ce ta yi “blocking” ɗin makanikin motarta (ta toshe shi) bayan ta lura cewa yana yawan kasancewa cikin mutanen farko da ke kallon Status ɗinta.
Zainab ta ce lamarin ya sa ta fara tunanin ko makanikin yana bibiyar ta ne tare hanyar abubuwan da take wallafawa a Status.
Ta ce ta kuma tuna wata rana da makanikin ya kira ta, inda bayan gaisuwa ya ce mata:
“Hajiya, wallahi, dole na tabbatar ’yata ta yi ilimi sosai kamar ke.”
Zainab ta ce lokacin da ta tambaye shi dalilin hakan, sai ya bayyana cewa yana son yadda take tafiyar da al’amuranta cikin tsari da kuma yadda take yin abubuwa yadda ya kamata.
Ta ce duk da cewa maganar ta mutunci ce, amma ba ta ji dadin maganar ba, domin a ganin ta bai dace makanikin ya riƙa kiranta ko tattaunawa da ita kan abubuwan da ba su shafi motarta ba.
Saboda haka, ta ce ta yanke shawarar yin “blocking” ɗinsa, tare da wasu mutane irin sa da ba ta ganin ya kamata su riƙa samun damar bibiyar abubuwan da take wallafawa.
“Ba kowa ya kamata ya riƙa bibiyar Status ɗinmu ba,” inji Zainab.
Ta kuma tambayi masu amfani da kafafen sada zumunta ko akwai waɗanda suka taɓa fuskantar irin wannan yanayi.




