Likitoci a Vietnam Sun Yi Nasarar Dashen Mazaƙuta ga Wani Namiji Mai Shekara 43 – an ciro daga wani mamaci aka dasa masa

DA DUMI-DUMI

Likitoci a ƙasar Vietnam sun samu nasarar gudanar da dashen mazaƙuta (azzakari) na farko a ƙasar ga wani mutum mai shekara 43, inda aka yi amfani da azzakarin wani mutum da aka tabbatar ya mutu, (brain-dead donor).

Mutumin ya rasa babban ɓangaren azzakarinsa bayan an yi masa tiyatar cire wani sashe (partial penectomy) shekaru huɗu da suka gabata a Asibitin Viet Duc Friendship da ke Hanoi. Duk da cewa yana iya yin fitsari yadda ya kamata, ƙaramin ɓangaren da ya rage ya jefa shi cikin damuwa.

Bayan gwaje-gwaje da suka haɗa da lafiyarsa, dacewar ƙwayoyin jiki (immune compatibility), yanayin tunaninsa da kuma la’akari da ƙa’idojin ɗabi’a, ƙungiyar ƙwararrun likitoci ta amince ya cancanci a yi masa dashen.

Daraktan Cibiyar Kula da Lafiyar Mazaje ta asibitin, Farfesa Nguyen Quang, ya ce likitocin sun sake gina muhimman sassan azzakarin tare da haɗa ƙananan jijiyoyin jini da jijiyoyin ƙwaƙwalwa ta amfani da fasahar tiyatar ƙananan jijiyoyi (microsurgery), aikin da ke buƙatar matuƙar ƙwarewa da daidaito.

A halin yanzu, likitoci sun ce marar lafiyar na samun sauƙi, kuma sabon azzakarin na warkewa yadda ake sa ran zai yi. Haka kuma zuwa yanzu, babu wata matsala da aka gani, yayin da yake amsa magungunan hana jiki ƙin karɓar sabon sashen.

Sai dai likitocin sun bayyana cewa har yanzu lokaci ne kawai zai nuna ko zai dawo da jin daɗinsa, ƙarfin tsayuwar mazaƙutar da kuma cikakken aikin yin fitsari, yayin da za su ci gaba da sanya ido kan yiwuwar jiki ya ƙi karɓar sabon sashen.

Shugaban asibitin, Dakta Duong Duc Hung, ya ce wannan shi ne dashen azzakari na farko da aka taɓa yi a Vietnam daga mai bayar da sashen jiki da ya mutu ta fuskar kwakwalwa. Ya ƙara da cewa ƙungiyar likitocin ta shafe watanni tana shirye-shirye tare da nazarin irin ayyukan da aka yi a wasu ƙasashe kafin gudanar da tiyatar.

Rahotannin likitanci na duniya sun nuna cewa kafin wannan nasara, an taɓa samun nasarar dashen azzakari sau biyar ne kacal a faɗin duniya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img