Gwamnatin Abia Ta Sanya Harajin Naira miliyan 200 da Miliyan 150 Ga Duk Dan takarar Shugaban Ƙasa da Gwamna Dake Son Saka Allon Takararsa a Jihar

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa duk ɗan takarar shugaban ƙasa da ke son kafa allunan yaƙin neman zaɓe (billboards) da fastoci a jihar zai biya Naira miliyan 200 domin samun lasisin yin hakan.

Hukumar Kula da Allunan Talla da Alamomin Kasuwanci ta Jihar Abia (ABSSAA) ce ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin Aba.

Shugaban Sashen Dabaru, Ƙirkire-ƙirkire da Tsara na hukumar, Ndubuisi Nwaogwugwu, ya ce jadawalin kuɗaɗen ya shafi dukkan ‘yan takara a matakai daban-daban. A cewarsa, ɗan takarar gwamna zai biya Naira miliyan 150, ɗan takarar Sanata Naira miliyan 100, ɗan takarar Majalisar Wakilai Naira miliyan 50, yayin da ɗan takarar Majalisar Dokokin Jiha zai biya Naira miliyan 20.

Darakta Janar na Ofishin Sadarwa na Gwamnatin Abia, Onyebuchi Ememanka, ya ce tsarin ba abin cece-kuce ba ne, yana mai cewa manufarsa ita ce tabbatar da tsaro, tsaftar muhalli da kuma gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin tsari. Ya kuma jaddada cewa gwamnati ba za ta nuna bambanci ga kowace jam’iyya ko ɗan takara ba, muddin an bi ƙa’idoji kuma an biya kuɗin da aka tanada.

Sai dai Ƙungiyar Masu Tallace-tallace ta Waje ta Najeriya (OAAN) ta nuna damuwa kan sabon jadawalin kuɗin, tana mai cewa kuɗaɗen sun yi tsauri kuma za su iya kawo cikas ga tallan siyasa a jihar.

Shi ma shugaban jam’iyyar ADC a Abia, Kalu Kalu, ya ce idan dokar jihar ta tanadi irin waɗannan kuɗaɗe jam’iyyarsa za ta biya. Amma idan ba haka ba ne, ya kamata a soke tsarin. Ya kuma yi nuni da cewa hukuncin Kotun Ƙoli ya bai wa ƙananan hukumomi ikon karɓar irin waɗannan kuɗaɗe, yana mai gargadin cewa duk wata doka da ta saɓa wa Dokar Zaɓe ba za ta dore ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img