Daga Wakiliya
Idan kana neman wayar Android mai kyamara mai inganci kamar ta iPhone 17, masana sun ce akwai wasu manyan wayoyi da za su iya yin gogayya da ita, har ma wasu sun fi ta a wasu fannoni.
Ga jerin wayoyin:
– Samsung Galaxy S26 Ultra – Tana da kyamara mai ƙarfi ta 200MP, kuma ta yi fice wajen ɗaukar hoto da bidiyo da kuma zoom mai nisa.
– Google Pixel 10 – Ta shahara wajen ɗaukar hotuna masu kyau da launuka na zahiri, tare da kyakkyawan zoom.
– Xiaomi 15 Ultra – An haɗa ta da fasahar Leica, tana ɗaukar hotuna masu inganci musamman da daddare.
– Vivo X300 Pro – Kyamararta da aka ƙera tare da ZEISS ta yi fice wajen hotunan mutum (portrait) da kuma bidiyo.
– OPPO Find X8 Pro – Tana ba da kyakkyawan hoto da bidiyo, musamman a wuraren da haske ya yi ƙasa.
– Honor Magic7 Pro – Ta yi fice wajen ɗaukar hotuna masu haske da cikakkun bayanai, musamman da daddare.
– OnePlus 13 – Haɗin gwiwarta da Hasselblad ya sa take ɗaukar hotuna masu launi na zahiri da inganci.
– Sony Xperia 1 VI – Ta fi dacewa da masu son sarrafa saitunan kyamara da kansu kamar yadda ake yi a kyamarorin ƙwararru.
Masana sun bayyana cewa duk da iPhone 17 na ci gaba da yin suna wajen ɗaukar bidiyo da sauƙin amfani da kyamara, wayoyin Android na zamani sun rage tazarar da ke tsakaninsu, kuma wasu ma sun zarce ta a fannoni kamar zoom, hotunan dare da kuma manyan na’urorin kyamara.





