Ku Harbe Duk Wanda Kuka Gani Da Bindiga Ba Bisa Ka’ida Ba – Sufeto Janar Na ‘Yan Sanda Ya Umarci Jami’ai

DA DUMI-DUMI

Sufeto Janar na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya umarci jami’an ‘yan sanda a fadin kasar nan da su harbe duk wanda aka samu dauke da bindiga ba bisa ka’ida ba, a wani sabon mataki na yaki da matsalar tsaro.

Disu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Jihar Benue da ke Makurdi.

Ya ce umarnin ya biyo bayan umarnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta addabi Jihar Benue.

Sufeto Janar din ya jaddada cewa jami’an tsaro da doka ta amince da su ne kawai ke da ikon daukar makamai, yana mai gargadin cewa ba za a ci gaba da kyale mutane suna yawo da bindigogi ba tare da izini ba.

A cewarsa, karkashin Force Order 237, an bai wa jami’an ‘yan sanda ikon daukar matakin gaggawa kan duk wani mutum da ke dauke da makami ba bisa ka’ida ba, ba tare da jiran umarni daga manyansu ba.

Haka kuma, Olatunji Disu ya bukaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanan sirri domin taimakawa wajen yaki da masu aikata laifuka.

Jihar Benue dai na ci gaba da fuskantar hare-haren masu dauke da makamai a watannin baya-bayan nan, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuka, raba mutane da muhallansu tare da lalata dukiyoyi. Gwamnatin Tarayya ta ce tana ci gaba da tura karin jami’an tsaro da daukar tsauraran matakai domin dawo da zaman lafiya a jihar.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img