Fassarar Ra’ayin Saddam Ibrahim
A Najeriya ana hasashen Musulmi sun haura miliyan 100. Tambayar da ya kamata mu fara yi wa kanmu ita ce: me muka yi da wannan adadin?
Shin mun gina al’umma mai ilimi? Mun rage talauci? Mun zama abin koyi a binciken kimiyya, fasaha, kasuwanci da shugabanci nagari? Ko kuwa har yanzu muna ta fafutukar ƙara lambobin mabiya ne kawai?
Yawan jama’a ba shi ne ma’aunin ƙarfi ba. Yahudawa ba su kai yawan al’ummar Kano ba, amma tasirinsu a fannin kimiyya, fasaha, kuɗi da siyasa ya mamaye duniya. China kuwa ta zama ƙasa mai ƙarfi ne saboda ta zuba jari a ilimi, masana’antu da bincike, ba saboda yawan jama’arta kaɗai ba.
Idan har muna son Musulunci ya ci gaba da samun daraja, abin da ya kamata mu fi mayar da hankali a kai shi ne gina Musulmi masu ilimi, masu sana’a, masu kirkire-kirkire, masu dogaro da kai da kuma masu amfani ga bil’adama.
Wa’azi yana da muhimmanci, amma gyaran rayuwar Musulmin da suke akwai ya fi buƙatar gaggawa. Al’umma ba ta bunƙasa da yawan mutane kaɗai; tana bunƙasa ne da ingancin mutanen da take da su.





