“Ku gasa masara, ku sayar da Kosai ko Ƙuli-ƙuli” – Remi Tinubu ta ba mata shawarar dogaro da kai

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce fara ƙananan sana’o’i kamar soya kosai, gasa masara da kuma sayar da ƙuli-ƙuli ba sa buƙatar kuɗi masu yawa.

A cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Remi Tinubu tana jawabi ga wata ƙungiyar mata inda ta ce gwamnati ta ƙarfafa ‘yan Najeriya ta hanyoyi daban-daban, ciki har da bayar da tallafin kuɗi ga mutane da dama.

Ta ce: “Fara kasuwancin sayar da kosai ba ya buƙatar kuɗi masu yawa. Haka nan gasa masara ko sayar da ƙuli-ƙuli ba sa buƙatar jari mai yawa. Mun ƙarfafa ‘yan Najeriya gwargwadon iko, mun ba mutane tallafi, ni ma na ba wasu da dama.” inji Remi

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img