Kotu ta ki bayar da belin El-Rufai bisa dalilin rashin lafiya, Ta ce takardar Asibitin da ya gabatar ba ta da inganci

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Babbar Kotun Jihar Kaduna ta sake yin watsi da bukatar bayar da belin tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai, a shari’arsa da ICPC

Mai shari’a D. H. Khobo ya yanke hukuncin ne bayan El-Rufai ya nemi a bayar da shi beli bisa dalilin rashin lafiya, yana mai gabatar da wata takarda da aka ce ta fito daga babban Asibitin Abuja, wato Abuja National Hospital.

Sai dai ICPC ta gabatar da martani daga Babban Daraktan Asibitin, Muhammad Raji Mahmud, wanda ya bayyana cewa binciken da aka yi bai gano wata shaida da ke nuna El-Rufai ya taba samun magani a asibitin ba, tare da cewa takardar ba ta samu amincewar mahukuntan asibitin ba.

Kotun ta ce bayan an karyata ingancin takardar, babu wata hujja mai karfi da za ta tabbatar da bukatar belin saboda rashin lafiya, don haka ta yi watsi da bukatar.

Sai dai kotun ta umarci ICPC da ta ci gaba da bai wa El-Rufai damar ganin likitocinsa tare da raka shi zuwa duk wata cibiyar lafiya ta musamman da ya zaba a cikin Najeriya idan bukatar hakan ta taso yayin da ake ci gaba da shari’ar.

ICPC ta ce ta yi maraba da hukuncin, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike da shari’o’inta cikin adalci da bin doka.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img