Gwamnatin Tarayya ta baiwa kamfanin Wutar China aikin wutar Mambila

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Tarayya ta baiwa kamfanin Wutar China aikin wutar Mambila

Daga Wakiliya

Gwamnatin Tarayya ta umarci kamfanin Energy China da ya sake duba hanyoyin da suka fi dacewa domin farfaɗo da aikin samar da wutar lantarki na Mambila, mai ƙarfin megawatt 3,050.

Wannan na zuwa ne bayan Najeriya ta yi nasara a shari’ar sasanta rikicin kwangilar aikin.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya ce ana duba yiwuwar kammala aikin a matakai domin tabbatar da aiwatar da shi cikin sauƙi.

Ya kuma ce Najeriya ta samu sabbin alkawura daga wasu kamfanonin China da masu bayar da kuɗaɗen ayyuka domin hanzarta manyan ayyukan wutar lantarki da layukan rarrabawa a ƙasar.

Daga cikin ayyukan akwai Presidential Power Initiative, aikin Zungeru, da shirin East-West Super Grid, wanda gwamnati ta ce za a aiwatar da shi cikin shekaru uku.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img