Daga Wakiliya
Ministan Matasa, Olawande Emmanuel Ayodele, ya bayyana cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta yanke hukunci kan sauya kayan sawa na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ba.
Ministan ya yi wannan karin haske ne bayan rahotannin da suka biyo bayan hirarsa da ya yi a tashar Channels TV, inda wasu suka fassara cewa an amince da amfani da kayan Adire ko Ankara a matsayin sabbin kayan NYSC.
A cewarsa, abin da ya yi shi ne bayar da misalan wasu shawarwari da aka gabatar yayin tattaunawar da ake yi kan sauye-sauyen shirin NYSC, ba sanar da cewa an amince da wani sabon zane ko nau’in kaya ba.
Ya ce gwamnati na nazarin zabuka daban-daban da za su tabbatar da ingancin kayan, dorewarsu, sauƙin amfani, rahusar farashi, da kuma wakiltar martabar Najeriya.
Ministan ya ƙara da cewa duk wani mataki da za a ɗauka zai biyo bayan cikakkiyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki, tare da la’akari da abin da ya fi dacewa da NYSC da ƙasar baki ɗaya.
Ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya su mayar da hankali kan manyan manufofin gyaran NYSC, waɗanda suka haɗa da inganta damar samun aiki ga matasa, ƙarfafa harkokin kasuwanci, bunƙasa haɗin kan ƙasa, da kuma inganta yadda shirin ke gudanar da ayyukansa.
A cewarsa, batun sauya kayan NYSC bai kamata ya mamaye muhimman sauye-sauyen da ake shirin aiwatarwa domin amfanin matasan Najeriya da ci gaban ƙasa ba.




