Ba ma goyon bayan tsarin tikitin Musulmi da Musulmi a Najeriya – Kwankwaso

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce har yanzu yana mamakin yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake gabatar da tikitin Musulmi da Musulmi domin zaɓen 2027.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a shirin Politics Today na tashar Channels TV, inda ya ce har yanzu akwai lokaci kafin ranar sauya sunayen ‘yan takara, don haka ya kamata Shugaba Tinubu ya zaɓi mataimaki daga wata addini domin a samar da daidaito.

Ya ce lokacin da yake neman mataimaki a zaɓen 2023, ya zaɓi wani babban limamin Kirista (Archbishop) domin kowa ya ji ana tafiya da shi.

Sai dai Kwankwaso ya jaddada cewa abin da ‘yan Najeriya, musamman matasa, ke buƙata a yanzu ba batun addini ko ƙabila ba ne, illa shugabanni da za su inganta tsaro, rayuwa da walwalar jama’a.

Ya kuma ce masu sukar tikitin haɗakar NDC ba su fahimci halin da ake ciki a Arewacin Najeriya ba.

Dangane da rahotannin da ke cewa an ambaci sunansa a wani kudirin doka da ake shirin gabatarwa a Amurka kan zargin take haƙƙin addini, Kwankwaso ya ce zarge-zargen siyasa ne kawai, yana mai cewa ba shi da wata kadara a wajen Najeriya da za a iya daskarar.

Game da ƙarar da ake yi kan jam’iyyar NDC, Kwankwaso ya bayyana kwarin gwiwar cewa kotu ba za ta hana jam’iyyar shiga zaɓen 2027 ba, yana cewa bai yi tsammanin wani alkali mai mutunci zai yanke irin wannan hukunci ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img