Daga Wakiliya
TABDIJAN: Kawu na ya bani Milyan Ɗaya Jari na cinye shine ya kira mini yan sanda -Me ya kamata na yi?
Daga Wakiliya
Wata matashiyar ‘yar Najeriya ta jawo ce-ce-ku-ce bayan ta kawo karar kawun ta Social media saboda a cewarta, ta karɓi rancen Naira dubu dari 800 daga kawun nata domin fara kasuwanci, amma kasuwancin ya rushe bayan watanni takwas.
Ta ce bayan ta sanar da shi halin da ake ciki, maimakon ya yi mata faɗa sai ya ƙara ba ta Naira dubu 200 yana mai cewa kada ta cire tsammani ta kara dagewa ta jaraba,
Sai dai, bayan ya kara mata dubu 200 sabon kasuwancin ma ya sake rushewa, ta ce da ta koma wurinsa karo na biyu, amma sai kawun nata ya kira mata jami’an ‘yan sanda.
Shine take tambayar ko ya ya za ta yi….?





