Da gangan El-Rufai ya shirya kashe mutanen Kudancin Kaduna — inji Honourable Christopher Musa

DA DUMI-DUMI

Da gangan El-Rufai ya shirya kashe mutanen Kudancin Kaduna — inji Honourable Christopher Musa

Daga Wakiliya

Babban Jigo a jam’iyyar APC kana kuma Ministan Tsaro na Najeriya, Honourable Christopher Musa, ya zargi tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da shirya kashe-kashen da aka yi wa mutane a Kudancin Kaduna da gangan.

Honourable Musa wanda tsohon Janar ne ya bayyana hakan ne a wata hira da shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV.

Jigon APCn ya ce gwamnatin El-Rufai ta taimaka wajen raba al’ummar Kaduna gida biyu, inda mutanen kudancin jihar ke fuskantar matsalar zama a arewacin jihar, haka kuma wasu daga arewa ke komawa kudanci.

Sai dai ministan ya ce gwamnatin gwamna Uba Sani ta yi kokarin dawo da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummar jihar.

A cewarsa Honourable : “El-Rufai ya yi abubuwa da dama marasa kyau a Kaduna. Ya raba jihar gida biyu.”

Da yake magana kan yadda mutanen Kudancin Kaduna ke kallon tsohon gwamnan, Janar Musa ya ce har yanzu suna cikin radadin kashe-kashen da aka samu a lokacin mulkinsa.

Ya zargi El-Rufai da cewa ya “shirya kashe mutanenmu da gangan”.

Ministan ya kuma yi ikirarin cewa tsohon gwamnan ya taba bayyana cewa ya biya ’yan bindiga, yana mai cewa El-Rufai bai ɓoye wasu daga cikin matakan da ya ɗauka ba.

Honourable Musa ya ce mutanen Kudancin Kaduna har yanzu suna cikin damuwa saboda kashe-kashen da suka faru a yankin, duk da cewa ya ce yanayin tsaro ya inganta a ƙarƙashin gwamnatin yanzu.

Ya kuma zargi tsohon gwamnan da hana wasu mutane damar samun wasu mukamai ko dama a lokacin mulkinsa.

Jigon APCn ya yi kira ga ’yan Najeriya da su guji zaɓar ’yan siyasar da ke amfani da addini ko ƙabila wajen raba kan jama’a.

Ya ce duk wanda ke amfani da bambancin addini ko ƙabila wajen raba Najeriya, ba mutum ne da ya kamata a ba amanar gwamnati ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img