Ba Ni Da Niyyar Yin Murabus – Babban Ministan Tsaro Ya Karyata Jita-jita

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Babban Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (Mai Ritaya), ya musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana shirin yin murabus daga mukaminsa.

A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar, an bayyana cewa rahotannin da ke cewa Janar Christopher Gwabin Musa zai sauka daga mukaminsa ƙarya ce tsagwaronta, wadda aka ƙirƙira domin yaudarar jama’a.

Sanarwar ta ce Babban Ministan Tsaron na ci gaba da gudanar da aikinsa ba tare da wata tangarda ba, kuma yana mai da hankali kan jagorantar manufofin tsaron ƙasa da kuma cika nauyin da aka ɗora masa.

Ofishin ya buƙaci jama’a su yi watsi da wannan jita-jita, tare da kira ga kafafen yaɗa labarai da masu amfani da kafafen sada zumunta su riƙa tantance sahihancin bayanai kafin yaɗa su.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img