Intanet ta zama sabon filin yaƙi da ‘yan ta’adda ke amfani da shi, suna ɗaukar sabbin mambobi da tara kuɗi

DA DUMI-DUMI

‘Yan ta’adda na amfani da intanet wajen ɗaukar sabbin mambobi, tara kuɗi – Rundunar Sojin Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta yi gargaɗin cewa ‘yan ta’adda da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka na ƙara amfani da intanet wajen ɗaukar sabbin mambobi, yaɗa farfaganda, tara kuɗi da kuma tsara hare-hare, lamarin da ta ce na ƙara barazana ga tsaron ƙasa.

Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana hakan a taron 2026 Nigerian Army Cyber Warfare School Seminar da aka gudanar a Abuja.

Ta bakin Mataimakin Babban Hafsan Sashen Ayyuka na Musamman, Manjo Janar Jeremiah Manjang, Shaibu ya ce intanet ta zama sabon filin yaƙi, inda maƙiya ke amfani da fasahar zamani ba tare da kasancewa a wurin ba wajen kai hare-hare, satar bayanai da yaɗa bayanan ƙarya.

Ya ce ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka na amfani da kafafen intanet wajen ɗaukar sababbin mambobi, tara kuɗi, tattara bayanan sirri da kuma ɓoye mu’amalolin kuɗaɗen da suka samu ta haramtacciyar hanya.

Shaibu ya ce hakan na buƙatar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro, masana da kamfanoni masu zaman kansu domin ƙarfafa tsaron yanar gizo da kare muhimman cibiyoyin Najeriya.

Ya kuma buƙaci a ƙara saka hannun jari wajen bunƙasa fasahar cikin gida, amfani da basirar wucin gadi (AI) da kuma horas da ƙwararrun ma’aikata domin ƙarfafa kariyar dijital da tsaron ƙasa.

Shi ma Kwamandan Nigerian Army Cyber Warfare School, Birgediya Janar Jacob Bawa, ya ce ƙaruwar amfani da fasahar dijital ta sa cibiyoyi masu muhimmanci kamar sadarwa, lantarki, bankuna da bayanan gwamnati suka fi fuskantar barazanar hare-haren intanet.

A nasa jawabin, ƙwararren masanin tsaron yanar gizo Abdulhakeem Ajijola ya ce Najeriya na buƙatar gina nata ƙarfin tsaron intanet, yana mai gargaɗin cewa dogaro da manhajoji da fasahohin ƙasashen waje kaɗai na iya zama barazana ga tsaron ƙasa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img