Bai kamata a samu ko yaro daya a Najeriya ya mutu saboda yunwa ba -inji Remi

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Remi Tinubu ta ƙaddamar da Bankin Abinci a Jigawa, ta ce bai kamata yaro ya mutu da yunwa ba

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da shirin Bankin Abinci na Ƙasa a Jihar Jigawa, inda ta ce babu wani yaro da ya kamata ya rasa ransa sakamakon yunwa ko rashin ingantaccen abinci.

Ta bayyana cewa shirin zai mayar da hankali ne wajen tallafa wa mata masu juna biyu, masu shayarwa da kuma yara masu ƙasa da shekara shida ta hanyar samar da abinci mai gina jiki a bankunan abinci da za a kafa kusa da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.

Oluremi Tinubu ta ce Shugaba Tinubu ya umarce ta da ta mara wa ƙoƙarin yaƙi da matsalar rashin abinci mai gina jiki baya a faɗin ƙasar.

A cewarta, rukunin  ya ba da gudummawar kayan abinci na darajar naira biliyan 20, yayin da  ke ɗaukar nauyin gina cibiyoyin bankin abinci a duk faɗin ƙasar kan naira biliyan 30. Ta kuma ce ita da kanta ta bayar da gudummawar naira miliyan 500 domin shirin.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img