Fiye da kashi 98% na masu ajiya a bankuna sun samu cikakken kariya idan banki ya rushe -NDIC

DA DUMI-DUMI


Daga Wakiliya


Hukumar Kula da Inshorar Ajiya ta Najeriya (NDIC) ta ce fiye da kashi 98 cikin 100 na masu ajiya a bankunan ƙasar yanzu suna ƙarƙashin cikakkiyar kariya idan banki ya gaza ko ya rushe.

Manajan Daraktan NDIC, Thompson Sunday, ya bayyana haka a ranar Litinin yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta shirya a Abuja.

Ya ce tun daga watan Mayun 2024 an ƙara adadin kuɗin da inshorar ajiya ke rufewa. A yanzu, masu ajiya a manyan bankuna za su samu kariya har zuwa Naira miliyan 5, maimakon Naira 500,000 da ake biya a baya.

Haka kuma, an ƙara iyakar kariya ga masu ajiya a bankunan ƙanana (Microfinance), bankunan gidaje (Primary Mortgage Banks) da bankunan biyan kuɗi (Payment Service Banks) zuwa Naira miliyan 2, yayin da masu amfani da Mobile Money su ma za su samu kariya har zuwa Naira miliyan 5.

A cewarsa, sabon tsarin ya tabbatar da cewa kashi 98.98% na duk masu ajiya a bankuna suna da cikakkiyar kariya, lamarin da zai ƙara amincewar jama’a da tsarin bankunan Najeriya tare da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img