Ina So In Raba Duka Dukiyata Kafin Na Mutu’ – Attajirin Amurka Denny Sanford Ya Rasu Bayan Ya Bayar da Fiye da Dala Biliyan 4 ga Ayyukan Jin Kai

Daga Wakiliya

Attajirin ɗan kasuwa kuma fitaccen mai ayyukan jin kai na Amurka, T. Denny Sanford, ya rasu yana da shekara 90 bayan ya shafe shekaru yana rabon mafi yawan dukiyarsa ga ayyukan alheri.

Sanford ya shahara da furucin da ya yi cewa: “Ina so na mutu ba tare da arziki ba.” A rayuwarsa, ya bayar da sama da dala biliyan 4 domin tallafa wa fannin lafiya, ilimi, binciken kimiyya da sauran ayyukan ci gaban al’umma.

Kimanin dala biliyan 2 daga cikin gudummawar tasa ya bai wa cibiyar lafiya da yanzu ake kira Sanford Health, wacce ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kiwon lafiya a yankunan karkarar Amurka.

Sanford ya fara rayuwa cikin talauci, amma ya tara dukiyarsa ne ta hanyar harkar banki, musamman kasuwancin katin bashi (credit cards), wanda ya sa ya zama ɗaya daga cikin attajiran Amurka.

Ko da yake sunansa ya taɓa shiga cikin binciken wata zargi a shekarar 2020, ba a gurfanar da shi a kotu ba bayan hukumomi suka ce ba su samu hujjar tuhuma a ƙarƙashin dokokin jiharsu ba.

Har zuwa rasuwarsa a ranar 18 ga Yuli, an kiyasta sauran dukiyarsa ta kai kusan dala biliyan 2.4, duk da cewa ya riga ya bayar da biliyoyin daloli domin amfanin al’umma.

#Wakiliya | Muryar Arewa a Duniya

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img