Na Yi Gwamna Tsawon Shekara Takwas Amma Ban Mallaki Ko Gidan Kaina ba – Aregbesola

DA DUMI-DUMI

Babban Sakataren jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, ya ce shi ne gwamna na farko a tarihin Najeriya da ya mulki jiha na tsawon shekara takwas ba tare da mallakar gida na kansa ba.

A cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ranar Alhamis, Aregbesola ya bayyana wa magoya bayansa cewa duk tsawon wa’adinsa na gwamnan Jihar Osun daga 2010 zuwa 2018, yana zaune ne a gidan wani abokinsa.

Ya ce, “Ni ne gwamna na farko a Najeriya da ya yi mulki na shekara takwas ba tare da mallakar gida na kansa ba. Na zauna a gidan abokina na tsawon shekara takwas ina gwamna a ƙasar mahaifina.

Duk wanda ya ce ba gaskiya nake faɗa ba, ya fito ya nuna gidan da na mallaka.”

Aregbesola ya kasance gwamnan Jihar Osun daga shekarar 2010 zuwa 2018, kafin daga bisani ya zama Ministan Harkokin Cikin Gida a gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

A lokacin mulkinsa, ya aiwatar da manufofi da suka mayar da hankali kan rage talauci da rashin aikin yi, inganta ilimi, lafiya, zaman lafiya da ci gaban al’umma.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img