Hukumar JSC Ta Tilasta Wa Alƙalin Kotun Shari’a a Kano Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin N250,000

Daga Wakiliya

Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kano (Judicial Service Commission – JSC) ta tilasta wa Alƙalin Kotun Shari’a da ke Babeji, Aliyu Yahaya Muhammad, yin ritaya bayan ta same shi da laifin karɓar cin hancin N250,000 a wata shari’a.

A cikin sanarwar da kakakin ma’aikatar shari’ar jihar, Baba Jibo Ibrahim, ya fitar, ya ce an yanke hukuncin ne a taron JSC na 90 bayan binciken Kwamitin Karɓar Korafe-korafen Jama’a ya tabbatar da zargin.

Hukumar ta kuma umarci Aliyu Yahaya Muhammad da ya mayar da kuɗin N250,000 da aka ce ya karɓa.

Haka kuma, magatakardar kotun, Ibrahim Ahmad Ibrahim, ya samu dakatarwa na tsawon watanni huɗu ba tare da albashi ba, bayan ya amsa cewa ya karɓi wani ɓangare na kuɗin cin hancin.

A wani hukuncin daban, JSC ta tilasta wa Muzambilu Ado, Mukaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a da Kididdiga na Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a, yin ritaya bayan bincike ya gano cewa ya gabatar da takardun karatu na bogi wajen samun aiki.

Sannan hukumar ta rage wa Alƙalin Babbar Kotun Shari’a ta Goron Dutse, Usman Haruna Usman, matsayi da mataki ɗaya saboda sakaci da ya haifar da asarar kuɗaɗen masu ƙara, tare da tabbatar da dakatarwar da aka yi masa na shekara guda daga aikin shari’a.

Baba Jibo Ibrahim ya ce matakan da aka ɗauka sun nuna ƙudirin JSC na tabbatar da gaskiya, riƙon amana da ɗa’a a harkokin shari’a, yana mai jaddada cewa duk wani jami’in shari’a da aka samu da laifin cin hanci ko amfani da ofis ba daidai ba zai fuskanci hukuncin da ya dace.

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img