Gwamnatin Tarayya Ta Fara Aiwatar da Sabuwar Dokar NIMC, Daga yanzu NIN Ce Kadai Shaidar Ɗan Ƙasa

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyarta ta aiwatar da sabuwar Dokar Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC) ta 2026, wadda ta tanadi amfani da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) a matsayin babbar kuma guda ɗaya da za a riƙa amfani da ita wajen tantance ‘yan Najeriya.

Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu, ya bayyana hakan yayin ganawa da Darakta Janar ta National Identity Management Commission, Abisoye Odusote, a Abuja.

Bagudu ya ce sabuwar dokar za ta ƙarfafa tsarin shaidar dijital na Najeriya, ta inganta shugabanci da kuma samar da ingantattun bayanai da za su taimaka wajen tsara manufofin ci gaba.

Ya kuma buƙaci haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi domin kawo ƙarshen yawaitar bayanan shaida daban-daban, tare da tabbatar da cewa NIN ta zama shaidar da za a amince da ita a ko’ina cikin ƙasar.

A nata ɓangaren, Darakta Janar ta NIMC, Abisoye Odusote, ta bayyana cewa sabuwar dokar ta soke wadda aka kafa a shekarar 2007, tare da tabbatar da tsarin “mutum ɗaya, shaida ɗaya”, sannan ta ƙara matakan kariyar bayanai da inganta tsarin dijital na ƙasa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img