Daga Wakiliya
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara “yaƙi” da abin da ya kira tsattsauran ra’ayin Musulunci, yana mai gargadin cewa duk malamin addini da ke yaɗa ra’ayoyin da gwamnati ta ɗauka a matsayin masu tsanani zai fuskanci matakin hukuma.
Traore ya ce, “Idan wannan ne Musuluncinku, za mu yaƙe shi. Masu tsattsauran ra’ayi su canza. Idan ba su canza ba, to yaƙin ya fara.
“Ya kuma kare sabuwar Dokar ‘Yancin Addini, wadda ya ce an kafa ta ne domin ƙarfafa tsarin ƙasa na rashin fifita wani addini (secularism).
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta iya dakatar da limaman da ke amfani da huɗubarsu wajen yaɗa abin da ta bayyana a matsayin tsattsauran ra’ayi.
Sai dai Traore ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa malaman Musulmi masu kira zuwa zaman lafiya, yana kuma zargin wasu ƙasashen waje da amfani da addini wajen haddasa rikici a Burkina Faso.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan rikici tsakanin gwamnati da wasu manyan malaman Musulmi ya ƙara tsananta.
A watan Mayu da ya gabata, jami’an tsaro sun kama fitaccen malamin Sunnah Imam Mohamed Ishaq Kindo, bayan ya soki kudirin Dokar ‘Yancin Addini. Hakan ya jawo zanga-zanga daga mabiyansa kafin gwamnati ta rufe babbar masallacin Sunnah da ke Ouagadougou saboda dalilan tsaro.
Rahotanni sun kuma ce kimanin mutum 100 daga cikin magoya bayan Imam Kindo an kai su sansanin soja domin abin da gwamnati ta kira horon ƙasa. Har yanzu dai cibiyar bincike ta Timbuktu Institute ta ce ba a san inda Imam Kindo yake ba.
Kafin haka ma, a watan Afrilu, an kama wani fitaccen malami, Imam Mahmoud Barro, a birnin Bobo-Dioulasso bisa irin wannan zargi.
Sabuwar dokar da majalisar riƙon ƙwarya ta amince da ita a ranar 20 ga Yuni ta tanadi hukuncin ɗauri da tara ga ayyukan da gwamnati ta bayyana a matsayin cin zarafin addini, ciki har da tilasta yara yin bara da kuma rashin bayyana yadda ƙungiyoyin addini ke sarrafa kuɗaɗensu.Masu sukar dokar dai na ganin gwamnati na ƙoƙarin ƙara ƙarfafa ikonta a kan cibiyoyin addini.
Traore ya kuma sanar da cewa za a ƙara sa ido kan ɗaliban Burkina Faso da ke zuwa ƙasashen waje domin karatun addinin Musulunci. Ya ce daga yanzu sai sun samu amincewar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi kafin tafiya, tare da gargadin cewa waɗanda suka ƙi komawa ƙasar bayan kammala karatu na iya rasa ɗan ƙasarsu.
A lokaci guda kuma, Burkina Faso na ci gaba da ƙarfafa alaƙarta da Isra’ila, bayan sabon jakadan Isra’ila a ƙasar, Simon Seroussi, ya gabatar da takardun shaidarsa ga Traore, yayin da ake ƙara haɗin gwiwa kan harkokin tsaro tsakanin Isra’ila da ƙasashen Alliance of Sahel States (AES).
Masana na gargaɗin cewa wannan sabon rikici da manyan malaman Musulmi na iya ƙara jefa gwamnatin Traore cikin ƙalubale, a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalar hare-haren masu iƙirarin jihadi da kuma matsin lambar siyasa.





