Al-Mustapha Ya Musanta Zargin Cewa Abacha Ya Mutu Tare Da Mace, Ya Ce Yana Da Duka Hotunan CCTV Na Abin da Ya Faru

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Tsohon Babban Jami’in Tsaron marigayi Shugaban Mulkin Soja, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya musanta ikirarin cewa Janar Abacha ya rasu ne yayin da yake tare da wata mace.

Al-Mustapha ya bayyana hakan ne a Kaduna yayin da yake mayar da martani kan zargin da tsohon jami’in Hukumar DSS, Dennis Amachree, ya yi a cikin wani littafi da ya wallafa.

A cewar Al-Mustapha, abin da Amachree ya rubuta ƙarya ce kuma ƙage ne, yana mai zargin cewa wasu ne suka rinjaye shi ya rubuta irin wannan bayani.

“An sa yaron ya rubuta waɗannan ƙaryoyin. Ina da dukkan hotunan CCTV na abin da ya faru a hannuna, don haka abin da ya faɗa ba gaskiya ba ne,” in ji Al-Mustapha.

Ya ƙara da cewa littafin bai bayyana gaskiyar abin da ya faru ba, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da wannan zargi.

Al-Mustapha ya ce bai dace a riƙa yaɗa zarge-zargen da ba su da tushe a kan mutumin da ya rasu, wanda ba zai iya kare kansa ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img