Ba na nadamar taimakon waɗanda a yanzu suka juya min baya domin dama ni don Allah nayi – El-Rufai
Daga Wakiliya
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ba ya jin ƙiyayya ko haushi ga mutanen da suka nisanta kansu da shi a lokacin da yake fuskantar ƙalubale.
El-Rufai ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken abota da abunda ya biyo baya, “My Relationships and the Aftermath”, da ya wallafa a shafinsa na intanet.
Ya ce a baya ya taimaki mutane da dama kuma ya yi hakan ne a bisa imaninsa, tarbiyyarsa a matsayinsa na dan Arewa da kuma abin da ya ga cewa shine ya dace, amma ba don neman suna ko su yi masa godiya ko tsammanin wani sakamako daga garesu ba.
Tsohon gwamnan ya ce wasu daga cikin mutanen na iya magana a kan halin da yake ciki, wasu kuma su yi shiru ko ma su nisanta kansu da dangantakar da ke tsakaninsu hakan ba zai dame shi ba.
Ya ƙara da cewa duk da abubuwan da suka faru, ba zai nemi ɗaukar fansa ko ramuwar gayya ba, yana mai cewa ya bar wa Allah komi shi zai saka masa kan duk wani zalunci ko cutarwa da aka yi mashi.
El-Rufai ya ce abin da ya fi damunsa a yanzu shi ne ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali da godiyar Allah sai kuma fatan gamawa da duniya lafiya.




