Firaministan Birtaniya Keir Starmer Ya Yi Murabus

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa na Firaminista da kuma shugaban jam’iyyar Labour.

A jawabin da ya gabatar a gaban gidan gwamnati na 10 Downing Street, Starmer ya ce ya fahimci cewa jam’iyyarsa ba ta ganin shi ne ya fi dacewa da jagorantar ta zuwa babban zaɓe mai zuwa.

Ya bayyana cewa zai ci gaba da riƙe mukamin har sai an zaɓi sabon shugaban jam’iyyar domin tabbatar da mika mulki cikin tsari.

Starmer ya gode wa iyalansa, musamman matarsa Victoria, tare da bayyana cewa nasarar dawo da Labour kan mulki ita ce mafi girman nasara a rayuwarsa ta siyasa.Rahotanni na nuna cewa Andy Burnham na daga cikin waɗanda ake hasashen za su maye gurbinsa a shugabancin jam’iyyar Labour.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img