KURI’A: Yawancin Yan Isra’ila Sun Ce Iran Ce Ta Yi Nasara a Rikicin Gabas ta Tsakiya

DA DUMI-DUMI

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a Isra’ila ta nuna cewa mafi yawan ‘yan kasar na ganin Iran ce ta fi cin moriyar rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma yarjejeniyar da ta kulla da Amurka.

Kuri’ar, wadda ta tattara ra’ayin mutane 3,644 tsakanin 17 zuwa 20 ga Yuni, ta nuna cewa kashi 92.1% na masu amsa tambayoyi sun ce Iran ce ta fi samun nasara ko riba daga rikicin.

Haka kuma, kashi 82.9% sun bayyana cewa tsaron Isra’ila na dogon lokaci ya samu rauni sakamakon rikicin.

Rahoton ya kuma nuna raguwar amincewa da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, inda kashi 72.5% suka ce ba su yarda da ikirarinsa kan nasarorin yakin ba.Sai dai duk da haka, kusan rabin masu amsa kuri’ar sun nuna goyon baya ga ci gaba da daukar matakin soja kan kungiyar Hezbollah a Lebanon.

A halin yanzu, ana sa ran Amurka da Iran za su ci gaba da tattaunawa a Switzerland domin mayar da yarjejeniyarsu ta wucin gadi zuwa ta dindindin.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img