El-Rufai bai ce ya yi kutse a wayar Ribadu ba -Adeyanju ya ba da shaida a Kotu

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake nuna bidiyon hirar tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya yi a Arise TV yayin da lauya kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Deji Adeyanju, ya bayar da shaida a shari’ar da Hukumar DSS ke yi masa.

Adeyanju ya shaida wa kotun cewa bidiyon ya nuna abubuwan da ya gani da kunnensa a shirin da aka gudanar ranar 13 ga Fabrairu, inda El-Rufai ya yi ikirarin cewa ya samu bayanai daga wata tattaunawar wayar tarho da ta shafi Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu.

A yayin tambayoyi daga lauyoyin ɓangarorin biyu, Adeyanju ya ce El-Rufai ya furta cewa “sun saurari kiran wayoyinsu”, amma bai ce da kansa ya yi kutse ko ya sace wayar ba.

DSS na tuhumar El-Rufai da laifin sauraron ko kutse cikin tattaunawar wayar Ribadu ba bisa ƙa’ida ba. Tsohon gwamnan ya musanta zarge-zargen kuma yana fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume guda biyar.Bayan kammala zaman ranar Litinin, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Talata domin ci gaba da shari’ar.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img