Hamshaƙin Attajirin Afirka Abdulsamad Rabiu Ya Mallaki Jirgin Sama Mafi Zamani Na Farko a Nahiyar
Daga Wakiliya
Shugaban Runkunin Kamfanonin BUA Group, Abdulsamad Rabiu, ya karɓi sabon jirgin sama na alfarma kirar Bombardier Global 8000, wanda ya zama jirgin sama irin sa na farko da aka kawo nahiyar Afirka.
Kamfanin Bombardier ya sanar da cewa jirgin ya fara aiki a ƙarƙashin BUA Group, Jirgin na Global 8000 na daga cikin jiragen kasuwanci mafi sauri da nisan tafiya a duniya. Yana iya yin tafiya kai tsaye daga Legas zuwa birane kamar Los Angeles, Tokyo da Perth ba tare da tsayawa don kara mai ba.
Rahotanni sun ce jirgin ya kai kimanin dala miliyan 81, yayin da farashinsa zai iya haura dala miliyan 95 idan aka yi masa ƙarin gyare-gyaren alfarma wato a takaice kusan Naira Biliyan 150bn a kudin Najeriya.

Masana sun bayyana cewa shigowar wannan jirgi Afirka na nuna yadda manyan ‘yan kasuwa da kamfanonin nahiyar ke ƙara shiga sahun masu amfani da sabbin fasahohin zirga-zirgar jiragen sama domin faɗaɗa harkokinsu a duniya.






