Da kafa Tinubu ke zuwa ofis, kuma sau ɗaya yake cin abinci a rana – Shugaban NRS, Zacch Adedeji
Daga Wakiliya
Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Najeriya (NRS), Zacch Adedeji, ya kare Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan zargin cewa gwamnatin tarayya na kashe makudan kuɗaɗe wajen gudanar da mulki.
Zacch Adedeji ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na rayuwa cikin sauƙin hali, inda ya ce shugaban kan tafi daga gidansa zuwa ofis da ƙafa, sai dai idan zai je filin jirgin sama.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels, wanda Seun Okinbaloye ke gabatarwa.
“Shugaban ƙasa yana tafiya daga gida zuwa ofis da ƙafa, ba ma ya shiga mota, sai dai idan zai je filin jirgin sama,” in ji shi.
Zacch Adedeji ya kuma tambayi masu sukar gwamnati kan amfani da motocin alfarma da jirgin shugaban ƙasa, yana cewa bai kamata a raina matsayin Najeriya ba.
Ya ce Shugaba Tinubu bai fita Najeriya ba tsawon watanni uku, yana mai cewa mafi yawan lokacinsa yana kan nazarin takardun gwamnati.
“Yana cin abinci sau ɗaya a rana. Sau nawa kuka gan shi yana liyafa a cikin shekaru uku?” in ji Zacch Adedeji.
Kan yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen gudanar da hukumomi da ma’aikatu, shugaban NRS ya ce bai kamata a rika kallon kuɗin da gwamnati ke kashewa kawai ba, domin akwai kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa da kuma kuɗaɗen da take samarwa ta hanyar waɗannan ayyukan.





