Nazari: Yadda rashin tsaro ke kara jefa yaran Arewa cikin matsalar rashin zuwa makaranta

Nazari: Yadda rashin tsaro ke kara jefa yaran Arewa cikin matsalar rashin zuwa makaranta

Daga Wakiliya

Rashin tsaro na kara jefa dubban yara a arewacin Najeriya cikin hadarin daina zuwa makaranta, yayin da hare-haren ‘yan bindiga da kungiyoyin ta'addanci ke tilasta rufe makarantu da kaura daga al'ummomi.

Masana ilimi da tsaro sun ce matsalar ba ta tsaya kan rasa darussa kawai ba.

Dr Obini Onuchukwu, shugaban Conference of Polytechnics and Colleges of Technology in Nigeria, ya ce dogon lokaci ba tare da zuwa makaranta ba na iya lalata tsarin karatun yara da kuma rage damar samun sakamakon ilimi mai kyau.

Ya ce yara ba sa iya cike gibin dogon rashin zuwa makaranta ta hanyar karatu a gida kawai, musamman idan ba su da kayan karatu da kulawar da ta dace.

Malamar ilimi Eloho Arhogho-Okeren ta ce wasu yara da suka bar makaranta na wani lokaci ba sa komawa, inda wasu ke shiga sana'o'in hannu, noma ko tallace-tallace.

Ta yi kira da a samar da darussan rediyo, cibiyoyin karatu ga al'umma, abinci a makaranta da shirye-shiryen dawo da yaran da suka rasa karatu.

Farfesa Al Chukwuma Okoli, masani kan harkokin tsaro, ya ce matsalar na iya kara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.

Ya ce yara da suka rasa ilimin farko na karatu da rubutu da lissafi na iya fuskantar matsaloli wajen samun aikin yi a nan gaba.

Ya kuma yi gargadin cewa yaran da ba sa makaranta na iya zama masu saukin fadawa hannun kungiyoyin ‘yan ta'adda, ‘yan bindiga da sauran kungiyoyin aikata laifuka.

A cewarsa, kare makarantu daga hare-hare ya kamata ya zama wani bangare na dabarun yaki da rashin tsaro.

DA DUMI-DUMI

Ana zargin Malam Jingir da amfani da addini wajen siyasa da rura ƙiyayya

Ana zargin Malam Jingir da amfani da addini wajen siyasa da rura ƙiyayya

Shan ruwan ’ya’yan itace (smoothie) a kullum na iya rage cutar damuwa (depression) – bincike

Saboda haka, suna ganin akwai buƙatar ƙarin bincike domin tabbatar da ko shan ruwan ’ya’yan itace a kai a kai na da tasiri kai tsaye wajen rage alamun damuwa. Binciken an wallafa shi a mujallar British Journal of Nutrition, kuma Fruit Juice Science Centre ce ta ɗauki nauyin gudanar da shi.

Da kafa Tinubu ke zuwa ofis, kuma sau É—aya yake cin abinci a rana – Shugaban NRS, Zacch Adedeji

Kan yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen gudanar da hukumomi da ma’aikatu, shugaban NRS ya ce bai kamata a rika kallon kuɗin da gwamnati ke kashewa kawai ba, domin akwai kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa da kuma kuɗaɗen da take samarwa ta hanyar waɗannan ayyukan.

Babu gaskiya a labarin cewa Sarki Sanusi ya samu ‘carry over’ — Masarautar Kano

Masarautar ta kuma ce bidiyon da ake yaɗawa an dauke shi ne yayin wani shiri da ɗaliban Shari’a suka gudanar, inda wasu matasa suka shirya shi da nufin yaɗa bayanan ƙarya.

Tinubu ya nemi haɗin kan Tijjaniyya wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi a Najeriya da yankin Sahel

Tinubu ya ce ya kamata malaman addini su riƙa jan hankalin shugabannin siyasa kan adalci, ɗaukar nauyi da tausayi, tare da jan hankalin jama’a da kada su mayar da ƙorafe-ƙorafe zuwa hujjar aikata rashin doka.

Kanun Labarai

Kalaman Jingir na da matuƙar tayar da hankali— Fani-Kayode ya caccaki malamin kan salon tallata tikitin Musulmi-Musulmi

A wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, Sheikh Jingir ya kuma yi kira ga Musulmi su mallaki katunan zaɓensu domin tunkarar zaɓen.

Har yanzu Atiku, da Obi da Kwankwaso na da damar hada kai domin kawar da Tinubu a 2027 -Ologbondiyan

Ya ce burin ADC shi ne samar da gwamnati da za ta yi aiki domin amfanin ’yan Najeriya tare da tabbatar da cewa dimokuradiyya ta amfani al’umma.

Duk wanda ya ce ’yan Najeriya na shan wahala ƙarƙashin Tinubu, ƙarya yake -Abu Ammar Shugaban Hisbah na Katsina

Duk wanda ya ce ’yan Najeriya na shan wahala ƙarƙashin Tinubu, ƙarya yake -mutanen da a baya ba sa iya sayen abinci yanzu suna iya saya -Abu Ammar Shugaban Hisbah na Katsina
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img