Ma’aikacin Jirgi Ibrahim Ya Mayar da Dalar Amurka 730 da Katunan Cire Kudi da Ya Tsinta a Yayin Goge Jirgi

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Ma’aikacin tsaftace cikin jirgin sama na kamfanin SAHCO, Ibrahim Bala Zakari, ya samu yabo bayan ya nuna gaskiya da rikon amana.

A yayin da yake tsaftace jirgin British Airways mai lamba BA8382, Zakari ya tsinci wata jaka a kujerar 35K wadda ke ɗauke da dala 730 (kimanin Naira miliyan 1.5) da kuma katunan cire kuɗi da dama,

Rahotanni sun ce nan take ya sanar da jami’in kula da ayyukan cikin jirgin na British Airways, inda daga bisani aka miƙa jakar tare da duk abin da ke cikinta ga sashen tsaro na kamfanin domin ci gaba da bin ƙa’idojin da suka dace.

Kamfanin SAHCO ya yabawa Ibrahim Bala Zakari, yana mai cewa abin da ya yi ya nuna gaskiya, rikon amana da ƙwarewar aiki, tare da bayyana shi a matsayin abin koyi ga sauran ma’aikata.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img