Daga Wakiliya
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da wani sabon tsari na gaggauta samar da ranar tattaunawar neman visa B1/B2, inda masu nema za su biya karin dala $750 domin samun ranar “Visa interview” cikin kwanaki 10.Sabon tsarin, wanda zai fara daga 1 ga Yuli zuwa 31 ga Disamba, 2026, zai gudana ne a wasu zaɓaɓɓun ofisoshin jakadancin Amurka da ofisoshin jakadunta.A halin yanzu, kudin neman visa na B1/B2 (kasuwanci da yawon buɗe ido) dala $185 ne kacal, yayin da za a biya karin dala $750 idan mutum ya zaɓi sabis na gaggawa.Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen ta bayyana cewa biyan wannan kuɗi ba ya tabbatar da cewa za a ba mutum visa.Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake fama da dogon lokacin jiran ranar “Visa Interview” a ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya, inda masu neman visa a Abuja ke jira kusan watanni 11 da rabi kafin samun rana.Har yanzu Amurka ba ta bayyana ofisoshin jakadancin da za su shiga wannan sabon shiri ba.




