Bayan Barazanar Ƙara, Fasto Primate Ya Janye Fatawar Cewa Kudi Kwankwaso Ya Karba Don Bata Zaben 2027

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya ce bai yi niyyar bata sunan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba, bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan hasashensa kan siyasar tsohon gwamnan Kano.

A baya, Ayodele ya yi hasashen cewa akwai rashin daidaito a dangantakar siyasar Kwankwaso da Peter Obi, tare da ikirarin cewa an rinjayi Kwankwaso da kuɗi ya amince ya zama mataimakin takarar shugaban ƙasa. Wannan hasashen ne ya sa Kwankwaso ya yi barazanar shigar da ƙarar neman diyyar Naira biliyan 10, yana zargin malamin da ɓata masa suna.

Sai dai a sabuwar sanarwar da ya fitar, Ayodele ya ce kalamansa hasashen da ya ce ya samu daga Allah ne kawai, ba wai zargi ko hari kan mutuncin Kwankwaso ba.

Ya ce bai taɓa haɗuwa da Kwankwaso ba, kuma babu wata matsala ta kashin kai da ke tsakaninsu. A cewarsa, an yi wa hasashensa mummunar fassara, yana roƙon duk wanda ya shafa da ya fara neman ƙarin bayani kafin ɗaukar matakin shari’a ko yin zarge-zarge.

Haka kuma, ya yi gargaɗi ga masu sauya ko yanke bidiyoyinsa domin cimma muradun siyasa ko na kashin kansu, yana mai cewa zai ɗauki mataki a kansu.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img