A Watan Yuni, Kuɗin Da Ke Hannun Jama’a Ya Ragu Da Naira Biliyan 486 A Najeriya – CBN

DA DUMI-DUMI

Kuɗin Da Ke Hannun Jama’a Ya Ragu Da Naira Biliyan 486 A Najeriya – CBN

 

Adadin kuɗin da ke hannun jama’a ba tare da an ajiye su a bankuna ba ya ragu zuwa Naira tiriliyan 4.92 a watan Yunin 2026, mafi ƙanƙanta cikin watanni bakwai, a cewar sabbin bayanan Babban Bankin Najeriya (CBN).

 

Bayanan sun nuna cewa kuɗin da ke wajen bankuna sun ragu daga Naira tiriliyan 5.41 a watan Disambar 2025 zuwa Naira tiriliyan 4.92 a watan Yunin 2026, raguwar da ta kai Naira biliyan 485.8, wato kusan kashi 9% cikin watanni shida.

 

Haka kuma, jimillar kuɗin da ke yawo a faɗin ƙasar ta ragu daga Naira tiriliyan 5.73 zuwa Naira tiriliyan 5.52 a daidai wannan lokaci.

 

Rahoton ya nuna cewa kusan kashi 89% na kuɗin da ke yawo a ƙasar har yanzu na hannun jama’a ne, yayin da sauran ke cikin tsarin bankuna.

 

CBN ya danganta wannan ci gaba da ƙoƙarinsa na ƙara yawan mutanen da ke amfani da harkokin kuɗi ta hanyar bankuna da kuma bunƙasa amfani da hanyoyin biyan kuɗi na zamani.

 

A lokacin ƙaddamar da shirin Payments System Vision 2028, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce bankin na da burin kai Najeriya ga kashi 95% na financial inclusion nan da shekarar 2028, tare da rage dogaro da kuɗin hannu.

 

Cardoso ya jaddada cewa manufar CBN ita ce kuɗin hannu su daina kasancewa hanyar biyan kuɗi mafi rinjaye, yayin da ake ƙarfafa biyan kuɗi ta hanyoyin dijital domin inganta tattalin arziki da kuma ƙara amincewar masu zuba jari.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img