An Kawo Ƙarshen Jita-jita: Tinubu Ya Sake Tsayar da Kashim Shettima a Matsayin Mataimakinsa

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Tinubu Ya Miƙa Takardar Tsayawa Takarar 2027, Ya Tabbatar da Kashim Shettima a Matsayin Mataimakinsa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa takardar tsayawa takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar APC ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), tare da tabbatar da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Ibrahim Kabir Masari, ne ya sanar da hakan tare da miƙa takardar tsayawa takarar Kashim Shettima a madadin shugaban ƙasa, yayin wani taƙaitaccen taro da ya samu halartar shugabannin APC a Continental Hotel da ke Abuja.

Da wannan mataki, Shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen jita-jitar da ta shafe watanni ana yaɗawa kan yiwuwar sauya Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img